1 Ku kasa kunne ga koyarwata, ya ku jama'ata,Ku kula da abin da nake faɗa.
2 Zan yi magana da ku,In faɗa muku asirai na dā,
3 Abubuwan da muka ji muka kuwa sani,Waɗanda kakanninmu suka faɗa mana.
4 Ba za mu ɓoye waɗannan abubuwa daga 'ya'yanmu ba,Amma za mu faɗa wa tsara mai zuwaLabarin ikon Ubangiji, da manya manyan ayyukansa,Da abubuwan banmamaki waɗanda ya aikata.