18 Da gangan suka jarraba Allah,Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.
19 Suka yi magana gāba da Allah, suka ce,“Ko Allah yana da iko ya ba mu abinci a hamada?
20 Gaskiya ce, ya bugi dutse,Ruwa kuwa ya fito a yalwace,Amma ko yana da iko ya ba da abinci da nama ga jama'arsa?”
21 Saboda haka Allah ya yi fushi sa'ad da ya ji su,Ya aukar wa jama'arsa da wuta,Fushinsa ya haɓaka a kansu,
22 Saboda ba su amince da shi ba,Ba su kuma gaskata yana da ikon cetonsu ba.
23 Amma ya yi magana da sararin sama,Ya umarci ƙofofinsa su buɗe,
24 Ya ba su tsaba daga sama,Da ya sauko musu da manna, su ci.