1 Ya Allah, arna sun fāɗa wa ƙasar jama'arka!Sun ƙazantar da Haikalinka tsattsarka,Sun bar Urushalima kufai.
2 Suka bar wa tsuntsaye gawawwakin jama'arka su ci,Suka bar wa namomin jeji gawawwakin bayinka.
3 Suka zubar da jinin jama'arka kamar ruwa,Jini ya yi ta gudu kamar ruwaKo'ina a Urushalima,Ba ma wanda ya ragu don yă binne gawawwaki.
4 Sauran al'ummar da take kewaye da mu,Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya,Suka yi mana ba'a.