3 Suka zubar da jinin jama'arka kamar ruwa,Jini ya yi ta gudu kamar ruwaKo'ina a Urushalima,Ba ma wanda ya ragu don yă binne gawawwaki.
4 Sauran al'ummar da take kewaye da mu,Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya,Suka yi mana ba'a.
5 Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji?Har abada ne?Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
6 Ka yi fushi da al'umman da ba su yi maka sujada,Ka yi fushi da jama'ar da suka ƙi ka!
7 Sun karkashe mutanenmu,Sun kuwa lalatar da ƙasarmu.
8 Kada ka hukunta mu saboda zunuban kakanninmu,Amma ka yi mana jinƙai yanzu,Gama mun fid da zuciya sarai.
9 Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,Saboda girmanka.Ka cece mu, ka gafarta mana zunubanmu,Don mutane su yabe ka.