1 Ya Ubangiji, Ubangijinmu,An san girmanka ko'ina a dukan duniya.Yabonka ya kai har sammai,
2 Yara da jarirai suna raira shi,Ka gina kagara saboda magabtanka,Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.
3 Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi,Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu,
4 Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi,Mutum kurum, har da kake lura da shi?