1 Ka kasa kunne gare mu, ya Makiyayin Isra'ila,Ka ji mu, kai da kake shugaban garkenka,Da kake zaune a kan kursiyinka, a bisa kerubobi.
2 Ka bayyana ƙaunarka ga kabilar Ifraimu,Da ta Biliyaminu, da ta Manassa!Ka nuna mana ikonka,Ka zo ka cece mu!
3 Ka komo da mu, ya Allah!Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!
4 Har yaushe ke nan ya Ubangiji Allah Mai Runduna,Za ka yi ta fushi da addu'o'in jama'arka?
5 Ka ciyar da mu da hawaye,Ka shayar da mu da babban ƙoƙo na hawaye.