2 Ka bayyana ƙaunarka ga kabilar Ifraimu,Da ta Biliyaminu, da ta Manassa!Ka nuna mana ikonka,Ka zo ka cece mu!
3 Ka komo da mu, ya Allah!Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!
4 Har yaushe ke nan ya Ubangiji Allah Mai Runduna,Za ka yi ta fushi da addu'o'in jama'arka?
5 Ka ciyar da mu da hawaye,Ka shayar da mu da babban ƙoƙo na hawaye.
6 Ka bar al'umman da take makwabtaka da muSu yi ta faɗa a kan ƙasarmu,Abokan gābanmu kuma suna yi mana ba'a.
7 Ka komo da mu, ya Allah Mai Runduna!Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!
8 Ka fito da kurangar inabi daga cikin Masar,Ka kori sauran al'umma,Ka dasa kurangar a ƙasarsu.