1 Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu,Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu!
2 A fara waƙa, ku buga bandiri,Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.
3 Ku busa ƙaho domin idin,A amaryar wata,Da a tsakiyar farin wata.
4 Wannan doka ce a Isra'ila,Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu.
5 Ya ba da wannan umarni ga jama'ar Isra'ila,A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar.Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa,