3 Ku busa ƙaho domin idin,A amaryar wata,Da a tsakiyar farin wata.
4 Wannan doka ce a Isra'ila,Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu.
5 Ya ba da wannan umarni ga jama'ar Isra'ila,A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar.Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa,
6 “Na ɗauke muku kayayyaki masu nauyi da kuke ɗauke da su a kā,Na sa kuka ajiye kwandunan aikinku.
7 Sa'ad da kuke shan wahalaKuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku.Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku,Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba.
8 “Ya kuma jama'ata Isra'ila ku kasa kunne,Ina kuwa so ku saurara gare ni.
9 Faufau kada ku bauta wa gumaka,Ko ku yi sujada ga wanina.