11 Ka yi wa shugabannin yaƙinsu yadda ka yi wa Oreb da Ziyib,Ka kori dukan masu mulkinsu yadda ka kori Zeba da Zalmunna,
12 Waɗanda suka ce, “Za mu ƙwace ƙasar da take ta Allah, ta zama tamu.”
13 Ya Allahna, ka warwatsa su kamar ƙura,Ka warwatsa su kamar ciyayin da iska take hurawa.
14 Kamar yadda wuta take cin jeji,Kamar yadda harshen wuta yake ƙone tuddai,
15 Ka runtume su da hadirinka,Ka razanar da su da iskarka mai ƙarfi.
16 Ya Ubangiji, ka sa kunya ta rufe su,Don su so su bauta maka.
17 Ka sa a kore su, a razanar da su har abada,Ka sa su mutu, mutuwar ƙasƙanci!