15 Ka runtume su da hadirinka,Ka razanar da su da iskarka mai ƙarfi.
16 Ya Ubangiji, ka sa kunya ta rufe su,Don su so su bauta maka.
17 Ka sa a kore su, a razanar da su har abada,Ka sa su mutu, mutuwar ƙasƙanci!
18 Ka sa su sani kai kaɗai ne Ubangiji,Kai kaɗai ne mamallakin dukan duniya!