3 Suna ta ƙulle-ƙulle a asirce gaba da jama'arka,Suna shirya maƙarƙashiya gāba da waɗanda kake tsaronsu.
4 Suna cewa, “Ku zo, mu hallakar da al'ummarsu,Don a manta da Isra'ila har abada!”
5 Suka yarda a kan abin da suka shirya,Suka haɗa kai gāba da kai.
6 Su ne mutanen Edom, da Isma'ilawa,Da mutanen Mowab, da Hagarawa,
7 Da mutanen Gebal, da na Ammon, da na Amalek,Da na Filistiya, da na Taya.
8 Assuriya ma ta haɗa kai da su,Haɗa kai ke nan mai ƙarfi da zuriyar Lutu.
9 Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa,Ka yi musu yadda ka yi wa SiseraDa Yabin a Kogin Kishon,