5 Suka yarda a kan abin da suka shirya,Suka haɗa kai gāba da kai.
6 Su ne mutanen Edom, da Isma'ilawa,Da mutanen Mowab, da Hagarawa,
7 Da mutanen Gebal, da na Ammon, da na Amalek,Da na Filistiya, da na Taya.
8 Assuriya ma ta haɗa kai da su,Haɗa kai ke nan mai ƙarfi da zuriyar Lutu.
9 Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa,Ka yi musu yadda ka yi wa SiseraDa Yabin a Kogin Kishon,
10 Waɗanda aka kora a Endor,Gawawwakinsu kuwa suka ruɓe a ƙasa.
11 Ka yi wa shugabannin yaƙinsu yadda ka yi wa Oreb da Ziyib,Ka kori dukan masu mulkinsu yadda ka kori Zeba da Zalmunna,