1 Ya Ubangiji, ka yi wa ƙasarka alheri,Ka sāke arzuta Isra'ila kuma.
2 Ka gafarta wa jama'arka zunubansu,Ka kuwa gafarta musu dukan kuskurensu,
3 Ka daina yin fushi da su,Ka kuwa kawar da zafin fushinka.
4 Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu,Ka daina jin haushinmu!
5 Za ka yi fushi da mu har abada?Ba za ka taɓa hucewa ba?