1 Ka kasa kunne gare ni, ya Ubangiji, ka amsa mini,Gama ba ni da ƙarfi, ba ni kuwa da mataimaki.
2 Ka cece ni daga mutuwa, saboda ni mai aminci ne a gare ka,Ka cece ni saboda ni bawanka ne, ina kuwa dogara gare ka.
3 Kai ne Allahna, saboda haka ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,Ina yin addu'a a gare ka dukan yini.
4 Ka sa bawanka yă yi murna, ya Ubangiji,Saboda addu'o'ina sun hau zuwa gare ka.