4 Ka sa bawanka yă yi murna, ya Ubangiji,Saboda addu'o'ina sun hau zuwa gare ka.
5 Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara,Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.
6 Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka ji kukana na neman taimako!
7 Nakan kira gare ka a lokacin wahala,Saboda kakan amsa addu'ata.
8 Ba wani allah kamarka, ya Ubangiji,Ba ko ɗaya, ba wanda zai iya aikata abin da kake aikatawa.
9 Dukan sauran al'umma da ka halittaZa su zo su rusuna har ƙasa a gabanka.Za su yabi girmanka,
10 Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah,Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.