5 Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara,Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.
6 Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka ji kukana na neman taimako!
7 Nakan kira gare ka a lokacin wahala,Saboda kakan amsa addu'ata.
8 Ba wani allah kamarka, ya Ubangiji,Ba ko ɗaya, ba wanda zai iya aikata abin da kake aikatawa.
9 Dukan sauran al'umma da ka halittaZa su zo su rusuna har ƙasa a gabanka.Za su yabi girmanka,
10 Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah,Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.
11 Ya Ubangiji, ka koya mini abin da kake so in yi,Ni kuwa zan yi maka biyayya da aminci.Ka koya mini in bauta maka da zuciya ɗaya.