9 Dukan sauran al'umma da ka halittaZa su zo su rusuna har ƙasa a gabanka.Za su yabi girmanka,
10 Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah,Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.
11 Ya Ubangiji, ka koya mini abin da kake so in yi,Ni kuwa zan yi maka biyayya da aminci.Ka koya mini in bauta maka da zuciya ɗaya.
12 Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji Allahna,Zan riƙa shelar girmanka har abada.
13 Wane irin girma madawwamiyar ƙaunarka take da shi a gare ni!Gama ka cece ni daga zurfin kabari.
14 Masu girmankai sun tasar mini, ya Allah,Ƙungiyar mugaye tana ƙoƙari ta kashe ni,Mutanen da ba su kula da kai ba.
15 Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna,Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.