1 Ya Ubangiji zan raira waƙarMadawwamiyar ƙaunarka koyaushe,Zan yi shelar amincinka a dukan lokaci.
2 Na sani ƙaunarka za ta dawwama har abada,Amincinka kuma tabbatacce ne kamar sararin sama.
3 Ka ce, “Na yi alkawari da mutumin da na zaɓa,Na yi wa bawana Dawuda alkawari cewa,
4 ‘Daga zuriyarka kullum za a sami sarki,Zan kiyaye mulkinka har abada.’ ”