28 Zan riƙa ƙaunarsa har abada,Alkawarin da na yi da shi kuma zai tabbata har abada.
29 A kullayaumin daga cikin zuriyarsa ne za a naɗa sarki,Mulkinsa zai dawwama kamar sararin sama.
30 “Amma idan zuriyarsa sun ƙi yin biyayya da shari'ata,Ba su kuwa zauna cikin ka'idodina ba,
31 In sun ƙyale koyarwata,Ba su kiyaye umarnaina ba,
32 To, sai in hukunta su saboda zunubansu,Zan bulale su saboda laifofinsu.
33 Amma fa, ba zan daina ƙaunar Dawuda ba,Ba kuwa zan rasa cika alkawarin da na yi masa ba.
34 Ba zan keta alkawarin da na yi masa ba,Ba zan soke ko ɗaya daga cikin alkawaran da na yi masa ba.