3 Ka ce, “Na yi alkawari da mutumin da na zaɓa,Na yi wa bawana Dawuda alkawari cewa,
4 ‘Daga zuriyarka kullum za a sami sarki,Zan kiyaye mulkinka har abada.’ ”
5 Talikan da suke Sama suna raira waƙa a kanAbubuwan banmamakin da kake yi,Suna raira waƙa kan amincinka, ya Ubangiji.
6 Ba wani kamarka a Sama, ya Ubangiji,Ba wani daga su cikin talikai da yake daidai da kai.
7 Ana girmama ka a cikin majalisar talikai,Duk waɗanda suke kewaye da kai suna yin tsoronka ƙwarai.
8 Ya Ubangiji Allah, Mai Runduna,Ba wani mai iko kamarka,Kai mai aminci ne a kowane abu.
9 Kai kake mulkin haukan teku,Kakan kwantar da haukan raƙuman ruwa.