35 “Da sunana mai tsarki na yi alkawari sau ɗaya tak,Ba zan yi wa Dawuda ƙarya ba!
36 Zuriyarsa za ta kasance kullum,Zan lura da mulkinsa muddin rana tana haskakawa.
37 Zai dawwama kamar wata,Kamar amintaccen mashaidin nan da yake a sararin sama.”
38 Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka,Ka rabu da shi, ka yashe shi.
39 Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka,Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.
40 Ka rurrushe garun birninsa,Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.
41 Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa,Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.