38 Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka,Ka rabu da shi, ka yashe shi.
39 Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka,Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.
40 Ka rurrushe garun birninsa,Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.
41 Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa,Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.
42 Ka ba maƙiyansa nasara,Ka sa dukansu su yi murna.
43 Ka sa makamansa su zama marasa amfani,Ka bari a ci shi da yaƙi.
44 Ka ƙwace masa sandan sarautarsa,Ka buge gadon sarautarsa ƙasa.