48 Wa zai rayu har abada, ba zai mutu ba?Ƙaƙa mutum zai hana kansa shiga kabari?
49 Ya Ubangiji, ina ƙaunarka ta dā?Ina alkawaran nan waɗanda ka yi wa Dawuda?
50 Kada ka manta da yadda aka ci mutuncina, ni da nake bawanka,Da yadda na daure da dukan cin mutuncin da arna suka yi mini.
51 Ya Ubangiji, kada ka manta da yadda maƙiyankasuka ci mutuncin zaɓaɓɓen sarki da ka naɗa!Suka yi ta cin mutuncinsa duk inda ya tafi.