16 Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari'arsa mai adalci,Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata.
17 Mutuwa ce maƙarar dukan mugaye,Da dukan waɗanda suke ƙin Allah.
18 Ba kullum ne ake ƙyale masu bukata ba,Ba za a danne sa zuciyar waɗanda ake zalunta ba har abada.
19 Ka zo, ya Ubangiji! Kada ka bari mutane su gagare ka!Ka kawo arna a gabanka, ka hukunta su.
20 Ka sa su ji tsoro, ya Ubangiji,Ka sa su sani su mutane ne kawai.