2 Zan raira waƙa da farin ciki sabili da kai,Zan raira yabo gare ka, ya Maɗaukaki!
3 Magabtana sun jā da baya da suka gan ka,Suka faɗi, suka mutu.
4 Kai da kake alƙali mai adalciKa zauna a kursiyinka,Ka kuwa yi shari'ar da ta yi mini daidai.
5 Ka kā da arna,Ka kuma hallakar da mugaye,Ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba.
6 An hallaka abokan gābanmu har abada,Ka lalatar da biranensu,An kuma manta da su sarai.
7 Amma Ubangiji sarki ne har abada,Ya kafa kursiyinsa domin yin shari'a.
8 Yana mulkin duniya da adalci,Yana yi wa mutane shari'a da gaskiya.