1 Ya Ubangiji, kai Allah ne wanda yake yin hukunci,Ka bayyana fushinka!
2 Kai ne mai yi wa dukan mutane shari'a,Ka tashi, ka sāka wa masu girmankaiAbin da ya dace da su!
3 Har yaushe mugaye za su yi ta murna?Har yaushe ne, ya Ubangiji?
4 Har yaushe za su yi shakiyanci,Su yi ta ɗaga kai?Har yaushe, ya Ubangiji?
5 Suna ragargaza jama'arka, ya Ubangiji,Suna zaluntar waɗanda suke naka.