13 Don ka ba shi hutawa a kwanakin wahala,Kafin a haƙa wa mugaye kabari.
14 Ubangiji ba zai rabu da jama'arsa ba,Ba zai rabu da waɗanda suke nasa ba.
15 Adalci kuma zai sāke dawowa cikin majalisun alƙalai,Dukan adalai kuwa za su yi na'am da shi.
16 Wa zai tsaya mini gāba da mugaye?Wa zai goyi bayana gāba da masu aikata mugunta?
17 Da ba domin Ubangiji ya taimake ni ba,Ai, da tuni na kai ƙasar da ba a motsi.
18 Na ce, “Ina kan fāɗuwa,”Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.
19 Sa'ad da nake alhini, ina cikin damuwa,Ka ta'azantar da ni, ka sa in yi murna.