3 Har yaushe mugaye za su yi ta murna?Har yaushe ne, ya Ubangiji?
4 Har yaushe za su yi shakiyanci,Su yi ta ɗaga kai?Har yaushe, ya Ubangiji?
5 Suna ragargaza jama'arka, ya Ubangiji,Suna zaluntar waɗanda suke naka.
6 Suna karkashe gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu,Da kuma baƙin da suke zaune a ƙasarmu.
7 Suna cewa, “Ai, Ubangiji ba ya ganinmu,Allah na Isra'ila ba ya lura da abin da yake faruwa!”
8 Ya jama'ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka?Sai yaushe za ku koya?
9 Allah ya yi mana kunnuwa, shi ba zai ji ba?Allah ya yi mana idanu, shi ba zai gani ba?