2 Mu zo gabansa da godiya,Mu raira waƙoƙin farin ciki na yabo!
3 Gama Ubangiji Allah ne mai iko,Shi yake mulki bisa sauran alloli duka.
4 Yana mulki bisa dukan duniya,Daga zurfafan kogwannin duwatsu zuwa tuddai mafiya tsayi.
5 Yana mulki bisa tekun da ya yi,Da kuma bisa ƙasar da ya siffata.
6 Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada,Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!
7 Shi ne Allahnmu,Mu ne jama'ar da yake lura da ita,Mu ne kuma garken da yake ciyarwa.Yau ku ji abin da yake faɗa.
8 “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.