4 Yana mulki bisa dukan duniya,Daga zurfafan kogwannin duwatsu zuwa tuddai mafiya tsayi.
5 Yana mulki bisa tekun da ya yi,Da kuma bisa ƙasar da ya siffata.
6 Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada,Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!
7 Shi ne Allahnmu,Mu ne jama'ar da yake lura da ita,Mu ne kuma garken da yake ciyarwa.Yau ku ji abin da yake faɗa.
8 “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.
9 A can suka gwada ni suka jarraba ni,Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.
10 A shekara arba'in ɗin nan,Jama'ar nan ta zama abar ƙyama gare ni,‘Su marasa biyayya ne,’ in ji ni,‘Gama sun ƙi bin umarnaina!’