1 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji!Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka!
2 Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi!Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa,“Ya cece mu!”
3 Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al'umma,Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai.
4 Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.
5 Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai,Amma Ubangiji ne ya yi sammai.