4 Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.
5 Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai,Amma Ubangiji ne ya yi sammai.
6 Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,Girma da jamali suna cikin Haikalinsa.
7 Dukan jama'ar da suke bisa duniya su yabi Ubangiji!Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!
8 Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka,Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.
9 Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa'ad da ya bayyana,Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka!
10 A faɗa wa dukan sauran al'umma, “Ubangiji Sarki ne!Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta,Ba za a iya kaushe ta ba,Shi zai shara'anta dukan jama'a da adalci.”