1 Ubangiji Sarki ne! Ki yi murna ke duniya!Ku yi murna, dukanku tsibiran da suke cikin tekuna!
2 Gajimare da duhu sun kewaye shi.A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.
3 Wuta tana tafe a gabansa, tana cinye maƙiyansaWaɗanda suke kewaye da shi.
4 Walƙiyarsa ta haskaka duniya,Duniya kuwa ta gani ta yi ta rawar jiki.
5 Tuddai sun narke a gaban Ubangiji kamar kākin zuma,A gaban Ubangijin dukan duniya.
6 Sammai suna shelar adalcinsa,Dukan kabilai kuwa, sun ga ɗaukakarsa.
7 Dukan waɗanda suke yi wa siffofi sujada za su sha kunya,Haka kuma waɗanda suke fāriya da gumakansu.Dukan alloli za su rusuna a gabansa.