4 Walƙiyarsa ta haskaka duniya,Duniya kuwa ta gani ta yi ta rawar jiki.
5 Tuddai sun narke a gaban Ubangiji kamar kākin zuma,A gaban Ubangijin dukan duniya.
6 Sammai suna shelar adalcinsa,Dukan kabilai kuwa, sun ga ɗaukakarsa.
7 Dukan waɗanda suke yi wa siffofi sujada za su sha kunya,Haka kuma waɗanda suke fāriya da gumakansu.Dukan alloli za su rusuna a gabansa.
8 Jama'ar Sihiyona suna murna,Garuruwan Yahuza kuma suna farin ciki,Sabili da irin shari'unka, ya Ubangiji!
9 Ya Ubangiji Mai Iko Dukka, kai kake mulkin dukan duniya,Ka fi sauran alloli duka girma.
10 Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta.Yakan kiyaye rayukan jama'arsa,Yakan cece su daga ikon mugaye.