20 Don ya ji nishin ɗaurarru,Don ya saki waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa.
21 Saboda wannan mutane za su yi shelar sunan Ubangiji a Sihiyona,Za su yi masa godiya a Urushalima,
22 Sa'ad da sauran al'umma da mulkoki suka taruDon su yi wa Ubangiji sujada.
23 Tun ina ƙaramin yaro Ubangiji ya sa na rasa ƙarfi,Ya gajerta kwanakina.
24 Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a yanzu,Tun da yake ban tsufa ba tukuna!Ya Ubangiji har abada kake.
25 Ka halicci duniya tun tuntuni,Da ikonka ne ka yi sammai.
26 Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama,Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa,Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.