24 Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a yanzu,Tun da yake ban tsufa ba tukuna!Ya Ubangiji har abada kake.
25 Ka halicci duniya tun tuntuni,Da ikonka ne ka yi sammai.
26 Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama,Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa,Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.
27 Amma kai, kana yadda kake kullayaumin,Har abada kake.
28 'Ya'yanmu za su yi zaman lafiya,Zuriyarsu kuma za su zauna cikin kiyayewarka kullayaumin.