1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!
2 Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!
3 Ku yi murna saboda mu nasa ne,Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!
4 Ku je wurin Ubangiji neman taimako,Ku tsaya a gabansa koyaushe.
5-6 Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu,Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.