42 Ya tuna da alkawarinsa mai tsarkiWanda ya yi wa bawansa Ibrahim.
43 Haka kuwa ya bi da jama'arsa, suka fita suna raira waƙa,Ya bi da zaɓaɓɓun jama'arsa, suna sowa ta farin ciki.
44 Ya ba su ƙasar baƙi,Ya sa su gāje gonakinsu,
45 Don jama'arsa su yi biyayya da dokokinsa,Su kuma kiyaye umarninsa.Ku yabi Ubangiji!