17 Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan,Ta binne Abiram da iyalinsa.
18 Wuta ta sauko bisa magoya bayansu,Ta ƙone mugayen mutanen nan.
19 Suka ƙera ɗan maraƙi da zinariya a Horeb,Suka yi masa sujada.
20 Suka musaya ɗaukakar AllahDa siffar dabba mai cin ciyawa.
21 Suka manta da Allah wanda ya cece su,Ta wurin manyan ayyuka da ya yi a Masar.
22 Kai, Allah ya aikata abubuwa masu ban al'ajabi a can!Ga kuma abubuwa masu banmamaki da ya aikata a Bahar Maliya!
23 Saboda wannan Allah ya ce zai hallaka jama'arsa,Amma Musa, zaɓaɓɓen bawansa, ya yi godo ga Allah,Allah kuwa ya huce, bai hallaka su ba.