21 Suka manta da Allah wanda ya cece su,Ta wurin manyan ayyuka da ya yi a Masar.
22 Kai, Allah ya aikata abubuwa masu ban al'ajabi a can!Ga kuma abubuwa masu banmamaki da ya aikata a Bahar Maliya!
23 Saboda wannan Allah ya ce zai hallaka jama'arsa,Amma Musa, zaɓaɓɓen bawansa, ya yi godo ga Allah,Allah kuwa ya huce, bai hallaka su ba.
24 Sai suka ƙi ƙasan nan mai ni'ima,Saboda ba su gaskata alkawarin Allah ba.
25 Suka zauna cikin alfarwansu suna ta gunaguni,Sun ƙi su saurari Ubangiji.
26 Saboda haka ya yi musu kakkausan kashedi,Cewa shi zai sa su duka su mutu a jejin,
27 Zai warwatsa zuriyarsu a cikin arna,Ya bar su su mutu a baƙuwar ƙasa.