36 Jama'ar Allah suka yi wa gumaka sujada.Wannan kuwa ya jawo musu hallaka.
37 Suka miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga allolin arna.
38 Suka karkashe mutane marasa laifi,Wato 'ya'yansu mata da maza.Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan'ana,Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.
39 Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu,Suka zama marasa aminci ga Allah.
40 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da jama'arsa,Ransa bai ji daɗinsu ba.
41 Sai ya bar su ƙarƙashin ikon arna,Abokan gābansu suka mallake su.
42 Abokan gābansu suka zalunce su,Suka tilasta su, su yi musu biyayya.