33 Ubangiji ya sa koguna suka ƙafe ƙaƙaf,Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.
34 Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani,Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.
35 Ya sāke hamada ta zama tafkunan ruwa,Ya kuma mai da busasshiyar ƙasa ta zama maɓuɓɓugai masu gudana.
36 Ya bar mayunwata su zauna a can,Suka kuwa gina birni don su zauna a ciki.
37 Suka shuka gonaki suka dasa kurangar inabi,Waɗanda suka ba da amfani mai yawan gaske.
38 Ya sa wa jama'arsa albarka,Suka kuwa haifi 'ya'ya da yawa.Bai bar garkunan shanunsu su ragu ba.
39 Sa'ad da aka ci nasara a kan jama'ar Allah,Aka ƙasƙantar da su ta wurin mugun zalunci,Da wahalar da aka yi musu.