14 Sai ka tuna, ya Ubangiji, da muguntar kakanninsa,Kada ka manta da zunuban mahaifiyarsa.
15 Ka tuna da zunubansu kullayaumin, ya Ubangiji,Amma su kansu a manta da su ɗungum!
16 Gama mutumin nan bai taɓa tunanin yin alheri ba,Yakan tsananta wa talakawa, da matalauta, da kasassu, har ya kashe su.
17 Yana jin daɗin la'antarwa, ka sa a la'anta shi!Ba ya son sa albarka, ka sa kada kowa ya sa masa albarka!
18 Yakan la'antar a sawwaƙe kamar yadda yake sa tufafinsa.Ka sa la'antarwa da yake yiSu jiƙa shi kamar ruwa,Su shiga har ƙasusuwansa kamar mai,
19 Su lulluɓe shi kamar tufa,Su kuma kewaye shi kamar ɗamara.
20 Ya Ubangiji, ka sa haka,Wato ya zama yadda za a hukunta wa maƙiyana ke nan,Waɗanda suke faɗar mugayen abubuwa a kaina!