7 Iyakar abin da yake yi duka, da aminci da adalci ne.Dukan umarnansa, abin dogara ne.
8 Sukan tabbata har abada,Da gaskiya da adalci aka ba da su.
9 Ya kawo wa jama'arsa ceto,Ya kuma yi musu madawwamin alkawari.Mai Tsarki ne shi, Maɗaukaki!
10 Hanyar samun hikima, ita ce tsoron Ubangiji,Yakan ba da kyakkyawar ganewaGa dukan waɗanda suke bin umarnansa,Sai ku yabe shi har abada!