1 Ku gode wa Ubangiji,Domin shi mai alheri ne,Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.
2 Bari jama'ar Isra'ila su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
3 Bari dukan firistoci na Allah su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
4 Bari dukan waɗanda suke tsoronsa su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
5 A cikin wahalata na yi kira ga UbangijiYa kuwa amsa mini, ya kuɓutar da ni.