3 Hakika ya aikata manyan al'amura sabili da mu,Mun kuwa yi farin ciki ƙwarai!
4 Ya Ubangiji, ka komar da mu ƙasarmuKamar yadda ruwan da kake yi yakan koma cikin busassun koguna,
5 Ka sa waɗanda suke kuka a lokacin da suke dashe,Su tattara albarkar kaka da farin ciki!
6 Su waɗanda suka yi kuka a sa'ad da suka fita suna ɗauke da iri,Za su komo ɗauke da albarkar kaka,Suna raira waƙa don farin ciki!