1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, mai kiyaye ni,Ya hore ni don yaƙi,Ya kuwa shirya ni don yaƙi.
2 Shi yake kiyaye ni,Shi yake kāre ni,Shi ne mafakata da Mai Cetona,Wanda nake dogara gare shiDon samun zaman lafiya.Shi ne ya ɗora ni a kan al'ummai.
3 Ya Ubangiji wane ne mutum, har da kake lura da shi?Wane ne ɗan adam kurum, har da kake kulawa da shi?
4 Shi kamar hucin iska yake,Kwanakinsa kuwa kamar inuwa mai wucewa ne.
5 Ya Ubangiji, ka kware sararin sama, ka sauko,Ka taɓa duwatsu, don su tuƙaƙo da hayaƙi.
6 Ka aiko da walƙiyar tsawa ta warwatsa maƙiyanka,Ka harba kibanka, ka sa su sheƙa a guje!
7 Ka sunkuyo daga Sama,Ka tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi, ka cece ni,Ka cece ni daga ikon baƙi,