7 Ka sunkuyo daga Sama,Ka tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi, ka cece ni,Ka cece ni daga ikon baƙi,
8 Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba,Sukan yi rantsuwar ƙarya.
9 Zan raira maka sabuwar waƙa, ya Allah,Zan kaɗa garaya in raira maka waƙa.
10 Ka ba sarakuna nasara,Ka kuma ceci bawanka Dawuda.
11 Ka cece ni daga mugayen abokan gābana,Ka ƙwato ni daga ikon baƙi,Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba,Sukan yi rantsuwar ƙarya.
12 Ka sa 'ya'yanmu maza waɗanda suke cikin samartaka,Su zama kamar itatuwan da yake girma da ƙarfi.Ka sa 'ya'yanmu mataSu zama kamar al'amudai,Waɗanda suke adanta kusurwoyin fāda.
13 Ka sa rumbunanmu su cikaDa kowane irin amfanin gona.Ka sa tumakin da suke cikin saurukanmuSu hayayyafa dubu dubu har sau goma,