1 Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina,Zan yi maka godiya har abada abadin.
2 Kowace rana zan yi maka godiya,Zan yabe ka har abada abadin.
3 Ubangiji mai girma ne, dole ne a fifita yabonsa,Girmansa ya fi ƙarfin ganewa.
4 Za a yabi abin da ka aikata daga tsara zuwa tsara,Za su yi shelar manya manyan ayyukanka.
5 Mutane za su yi magana a kan darajarka da ɗaukakarka,Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.